in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta kaddamar da yaki kan Falasdinawa, inji shugaba Abbas
2014-07-10 14:55:42 cri
A ranar jiya Laraba ne aka shiga yini na biyu tun bayan da sojojin Isra'ila suka fara kaddamar da hare-hare da yankunan al'ummar Falasdinawa, bisa abin da suka kira kiyaye tsaron iyakar kasar Isra'ila.

Wannan mataki dai ya sha suka daga shugaban Palesdinu Mahmoud Abbas, wanda ya zargi kasar Isra'ila da kaddamar da matakan soja don yakar al'ummar Palesdinu.

Abbas wanda ya kira taron gaggawa na kusoshin Falasdinawa, domin tattauan tasirin da wadannan matakan soja ka iya yi ga dangantakar dake tsakanin Isra'ila da Palesdinu, ya yi fatan ganin matsin lamba daga kasashen duniya kan Isra'ila, domin tilasata mata kawo karshen matakan sojan da ta ke dauka cikin hanzari.

A nasa bangare, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayar da wata sanarwa, inda ya ce, sojojin Isra'ila za su ci gaba da kai farmaki ga kungiyar Hamas da sauran dakarun da ke zirin Gaza.

A hannu guda kuma, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubale mafi tsanani a sakamakon rikicin da ya kunno kai a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Mr. Ban ya yi kira ga bangarori daban daban da wannan lamari ya shafa, da su yi kokari tare wajen daukar matakan warware matsalar bangarorin biyu a siyasance, tare da kuma dakile tsanantar rikicin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China