in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a daidaita rikicin Palestinu da Isra'ila cikin lumana
2014-07-11 20:43:59 cri
A Jumma'an nan 11 ga wata, a gun taron manema labaru da aka shirya, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Qin Gang ya bayyana cewa, kamata ya yi a daidaita wannan baturikicin da ya kasance tsakanin Palestinu da Isra'ila cikin lumana.

A yayin da yake amsa tambayar 'manema labarai dangane da yanayin da ake ciki na rikicin Palestinu da Isra'ila, Qin ya ce, kasar Sin bata jin dadin labarin rasuwan matasa Yahudawa 3 da wani dan Palestinu ba a kwanakin baya. Sai dai kuma wannan zai sa a kara bakin ciki idan mafi yawan mutane fararen hula suka mutu a sakamakon hakalamarin. A don haka Mr Qin ya ce, Sin tana mai da hankali da kuma damuwa sosai kan tsanantar rikicin Palestinu da Isra'ila, wadda kuma take ci gaba da haddasa mutuwar mutane da yawa, yayin da wasu suka jikkata. Kasar Sin ba ta yi aminceamincewa da duk wani hare-haren da ake kai wa fararen hula ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China