in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kiraye-kiraye ga Isra'ila da Palasdinu da su tsagaita bude wuta
2014-07-21 14:17:46 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya fidda wata sanarwa a kasar Qatar, inda ya yi tir da hare-haren da kasar Isra'ila ke kaiwa ta kasa a zirin Gaza, hare-haren da suka haddasa asarar rayuka da jikkatar fararen hula da dama. Mr. Ban ya fidda wannan sanarwa ne a jiya Lahadi lokacin da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Qatar.

A kuma wannan rana ita ma kakakin ofishin hukumar harkokin wajen kasar Amurka Jen Psaki, ta ce babban sakataren harkokin wajen Amurkan John Kerry zai halarci birnin Alkahira na kasar Masar a Litinin din nan, domin gudanar da shawarwari da masu ruwa da tsaki kan rikicin da ke wakana tsakanin Isra'ila da Palesdinu. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China