in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren kungiyar LAS ya yi tir da harin da sojojin kasar Isra'ila suka kai ga unguwar fararen hula dake zirin Gaza
2014-07-21 10:07:46 cri
Babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa wato LAS Nabil el-Araby ya bayar da wata sanarwa a ranar 20 ga wata, inda ya yi tir da harin da sojojin kasar Isra'ila suka kai ga unguwar fararen hula dake gabashin zirin Gaza wanda ya haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama, kana ya yi kira ga kasar Isra'ila da ta dakatar da daukar matakan sojan da take yi cikin hanzari.

An shiga hali mai tsanani kan rikicin dake tsakanin Palesdinu da Isra'ila a ranar 20 ga wata. Inda sojojin kasar Isra'ila sun kai hari ga wata unguwar fararen hula dake zirin Gaza a wannan rana, wanda ya haddasa mutuwar Palesdinawa 60 kana kimanin 400 sun ji rauni. Wannan ne mutuwa da raunatar mutane mafi yawa tun bayan da sojojin Isra'ila suka kai hari ta kasa kan zirin Gaza a ranar 17 ga wata. A kwana daya kawai wato ranar 20 ga wata, Palesdinawa fiye da 100 sun mutu a sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai kan zirin Gaza. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China