Sin ta sake yin kira da a dakatar da musayar wuta tsakanin Isra'ila da Falesdinu ba tare da bata lokaci ba
A kwanakin baya ne kasar Masar ta gabatar da kiran da a dakatar da bude wutan da ake tsakanin Isra'ila da Falesdinu, amma har yanzu ana ci gaba da musayar wuta sabo da kungiyar Hamas ta ki amince da wannan kiran. Tuni Isra'ila ta fara kai hare-hare ta kasa a yankin Gaza, don lalata hanyoyin karkashin kasa da Hamas ke amfani da su wajen shiga yankin Isra'ila .
Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yau Jumma'a 18 ga wata cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu ga bangarorin biyu shi ne a dakatar da rikice-rikicen dake tsakaninsu nan da nan bisa kiran gamayyar kasa da kasa, tare da hana ci gaba da daukar ko wane irin mataki da zai haddasa karin tabarbarewar yanayi dake tsakaninsu. (Maryam)