A ran 12 ga wata a birnin Kudus, jama'ar kasar Isra'ila sun nuna juyayi ga tsohon firaministan kasar Ariel Sharon, wanda ya rasu ba da dadewa ba.
A ran nan an ajiye akwatin da ke dauke da gawarsa a maharabar majalisar dokoki, an rufe akwatin da tutar kasar Isra'ila. Shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres, da shugaban majalisar dokoki Yuli Edelstein bi da bi ne suka ba da furanni, majalisar ta soke dukkan tarurruka, an saukar da tuta zuwa rabin sanda. Jama'ar Isra'ila fiye da dubu sun zo daga wurare daban daban don yi masa juyayi, sun yaba wa Sharon a matsayin wani mutum mai girma da aka yi hasara daga bangaren siyasa na Isra'ila, da wani soja mai girma da ke kokartawa a duk rayuwa don kasarsa.
A ran 13 ga wata da safe, Isra'ila zai shirya wani bikin ta'aziyya a matsayin kasa ga Sharon a babban ginin majalisar dokokin kasa. Shugaba Shimon Peres, da firaminista Benjamin Netanyahu na kasar Isra'ila, da mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, da tsohon firaministan kasar Britaniya Tony Blair da dai sauran shugabannin siyasa na kasa da kasa za su halarci bikin, bayan haka kuma sojoji za su kare gawar Sharon zuwa filin gona na Sycamore mallakar iyalinsa da ke kudancin kasar, inda za a binne shi.
A ran 11 ga wata, Sharon ya rasu a wani asibitin da ke birnin Tel Aviv, wanda shekarunsa ya kai 85 a duniya.(Danladi)