A ranar Litinin din nan ne ake gudanar da wasu shagulgula a kasar Israila, domin tunawa da jaruman kasar, da sauran 'yan mazan jiya wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar kisan gillar da aka kai musu.
An dai kaddamar da shagulgulan ne a daren jiya Lahadi a wani gidan ajiye kayayyakin tarihin kisan gilla na Yad Vashem.
Baban taken bukukuwan na wannan shekara dai shi ne, Yahudawa a shekara ta 1944, bisa hadarin kare dangi da kokarin samun 'yanci'.
Shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres, da firaministan kasar Benjamin Netanyahu sun halarci bikin tare da gabatar da jawabai. A kuma Ltitinin din nan za a ci gaba da shirya bukukuwa a wurare daban daban cikin kasar, duk dai da nufin tunawa da tarihin kisan gilla, da karrama 'yan mazan jiyan kasar. (Danladi)