Bisa labarin da sojojin Isra'ila suka bayar, an ce da sanyin safiya ranar 29 ga wata, an jefa ma yankin arewacin kasar Isra'ila rokoki daga wajen Lebanon, cikinsu, akwai rokoki guda 2 da suka fada a cikin iyakar kasar, duk da haka, lamarin bai kawo mutuwar kowa ba kuma ba wanda suka jikkata ba, don ta mayar da martani, sojojin Isra'ila suka kai harin bom sama da 10 ga kasar Lebanon. A wannan rana, ministan tsaro na Isra'ila Moshe Ya'alon ya bayyana cewa, ba zai amince da harin roka da aka kai a kasar daga kasar Lebanon ba, dole ne gwamnatin Lebanon ta dauki nauyin wannan lamari, in ba haka ba, sojojin Isra'ila za su yi ramuwar gayya.
A ranar 29 ga wata, kwamandan sojojin wucin gadi na M.D.D. da ke yankin kudancin kasar Lebanon Paolo Serra ya jaddada cewa, a wannan rana, harin roka da aka kai daga kudancin kasar Lebanon zuwa kasar Isra'ila yana da hadari sosai, kuma babban makasudin daukar wannan mataki shi ne, don lahanta aikin zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya. Ya bayyana cewa, yanzu sojojin M.D.D. dake kasar Lebanon suna daukar matakan tsaro tare da sojojin kasar, don tabbatar da wuraren da aka kai hari, da gurfanar da masu laifi gaban kuliya.
A ranar 29 ga wata, Babban magatakardan M.D.D. Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi Allah-wadai da harin rokar da aka kai, tare da yin kira ga bangarorin da abin ya shafa da su kai zuciya nesa. (Bako)