Ma'aikatar tsaron kasar Isra'ila ta bayar da wata sanarwa cewa, sakamakon tashe-tashen hankali tsakanin Isra'ila da Palesdinu, ya sanya kasar Isra'ila kara tura sojojinta a yankin zirin Gaza a ranar 3 ga wata.
Kakakin sojojin Isra'ila Peter Lerner ya bayyana a cikin sanarwar cewa, kara tura sojojin Isra'ila na da nasaba kai tsaye da wayan rakokin da aka harba daga zirin Gaza zuwa Isra'ila a cikin awoyi 48 da suka gabata. Isra'ila ta dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaron biranen Isra'ila da kuma al'ummominta.
A ranar 3 ga wata, kakakin kungiyar Hamas, Sami Abu-Zuhri ya ce, dole Isra'ila ta dauki alhakin tashe-tashen hankalin dake faruwa a zirin Gaza. Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu dai Hamas ba ta son tada rikici da Isra'ila, amma ya jaddada cewa, kungiyar Hamas a shirye take a ko wane lokaci kuma tana da kwarewa wajen tinkarar hare-haren Isra'ila kan zirin Gaza. (Danladi)