A wakiltar gwamnatin kasar Sin da jama'arta, shugaba Xi ya bayyanawa shugabannin biyu kyakkyawan fatan alheri, inda ya ce, shekaru 60 da suka gabata, kasashen uku sun daddale wadannan manufofi biyar. Zuwa yanzu, ana tunawa da wannan rana mai muhimmanci tare da jama'ar kasa da kasa. Wadannan manufofi sun kasance babban ci gaban da aka samu a karni na 20. A cikin shekaru 60 da suka shude, an dudduba su da aiwatar da su yadda ya kamata, wadanda suka samun amincewa daga kasashen duniya, kuma sun zama ka'idoji masu tushe da kasashen duniya suke bi, abin da ya ba da gudunmawa ga zaman lafiyar duniya da ci gaban Bil Adam. Kuma hakan ya bayyana wani matsayi mai karfi sosai yayin duniya ke fuskantar sauye-sauye, wanda kuma zai ba da sabuwar gudunmawa wajen kafa wata sabuwar dangantakar kasa da kasa dake nuna daidaici da adalci da amincewa da juna, da yin hakuri da juna tare da kawo moriyar juna.
Ban da haka kuma, Mr Xi yana fatan hadin gwiwa da kasashen duniya domin yada wadannan manufofi da daukacin duniya. (Amina)