Bisa bukatun MDD, nan gaba kadan gwamnatin kasar Sin za ta tura wani rukunin 'yan sanda kiyaye zaman lafiya masu aikin kwantar da tarzoma dake kunshe da mutane 140. Ma'aikatar tsaron lafiyar jama'a ta yi wani biki a ran 29 ga wata domin tura wadannan 'yan sanda zuwa Laberiya. Da safiyar yau Litinin 30 ga wata ne, rukunin ya tashi daga babban filin saukar jiragen sama dake nan birnin Beijing. Wannan ya kasance karo na farko da Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya dake aikin kwantar da tarzoma bisa tsari zuwa nahiyar Afirka.
Bayan da kungiyar share fage, za ta dauki nauyin gudanar da aikin karbar kayayyaki, gyara sansani, da tuntuba da sassan kasashen waje, abubuwan da suka yi sun aza tunbali ga manyan runkunonin da za su zo nan gaba.
A kwanaki masu zuwa ne ake sa ran rukuni na farko zai tashi zuwa wurin da zai gudanar da aikin nasa. (Amina)