A jawabin sa Li ya nuna cewa, ya kamata kasa da kasa su hada kansu don neman samun zaman lafiya da na tsaro, da tinkarar kalubaloli gaba daya domin ciyar da sha'anin zaman lafiya da bunkasuwa na bil Adama gaba.
Dandalin tattaunawar kan zaman lafiya shi ne dandalin farko na babban matsayi da kasar Sin ta shirya kan batun tsaro, amma ba na gwamnati ba. babban taken dandalin shi ne "Neman samun zaman lafiya da bunkasuwa da kirkire-kirkire kan batun tsaro a cikin juyin juya hali da duniya ke ciki".
Mataimakin Shugaban kasar na Sin Li Yuanchao ya kuma furta cewa, ya kamata kasa da kasa su yi zaman lafiya, da kuma warware rikice-rikice cikin ruwan sanyi, a kokarin kiyaye zaman lafiya na shiyya-shiyya da na duniya gaba daya. A don haka Kasar Sin a tsaye take tsayin daka kan bin hanyar samun ci gaba cikin lumana. Tana fatan kasa da kasa za su bi irin wannan hanya domin samar da kyakkyawar makoma ga sha'anin zaman lafiya da bunkasuwa na bil Adama.(Kande Gao)