Ya kamata a kara sanimmu game da "sanarwar Alkahira" da dai sauran yarjejeniyoyin kasa da kasa, in ji masanin Sin
Kwanan baya, shugaban cibiyar nazarin Asiya ta Gabas ta jami'ar Renmin ta kasar Sin Huang Dahui ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Japan tana kalubalantar "sanarwar Alkahira" da dai sauran yarjejeniyoyin da suka tsayar da ka'idojin kasa da kasa bayan babban yakin duniya na biyu. A watan Satumba na shekarar 2012, gwamnatin kasar Japan ta kulla wata yarjejeniyar sayan tsibirin Diaoyu da "mai mallakar tsibirin", sa'an nan ta sanar da mallakarta kan tsibirin. Matakin da kasar Japan ta dauka ya keta ikon kasar Sin kan yankin kasarta, kuma ya kawo barazana ga ka'idojin kasa da kasa da aka tsara bayan yakin duniya na biyu da kuma nasarar da aka cimma a yakin duniya na biyu.
Mr. Huang ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu, masu tsatsauran ra'ayin kasar Japan suna kalubalantar zaman lafiyar kasa da kasa, shi ya sa, don kiyaye 'sanarwar Alkahira' da kuma nasarar a yakin duniya na biyu, ya kamata kasashen Sin, Amurka da Burtaniya da suka tsara "sanarwar Alkahira" da dai sauran yarjejeniyoyin da abin ya shafa su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kuma dukufa wajen karfafa fahimtar gamayyar kasa da kasa kan yarjejeniyoyin don kiyaye ka'idojin sanarwar da sauran yarjejeniyoyi yadda ya kamata. (maryam)