A ranar Laraba da dare, agogon kasar Sin ne rukuni na 16 na dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka tashi zuwa kasar Liberia.
Tawaga ta farko mai kunshe da dakaru 558 daga bataliyar soja da ke birnin Beijing ta tashi ne daga filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke nan birnin Beijing. Yayin da ake sa ran tashin kashi na biyu na tawagar a ranar 29 ga watan Maris.
Tawagar wadda za ta shafe watanni 8 tana aiki kamar yadda MDD ta bukata, za ta gudanar da ayyukan da suka shafi sufuri, aikin injiniya, da kuma lafiya.
A watan Disamban shekarar 2003 ne kasar Sin ta fara tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar ta Liberia. (Ibrahim)