in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son kara bayar da gudummawa ga zaman lafiya a duniya
2013-12-12 10:01:50 cri

Ministan harkokin kasashen waje na kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a ranar Laraba cewa, kasarsa za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta na diflomasiya bisa tsarinta na musamma a shekara ta 2014 mai kamawa, yayin da take bayar da nata tallafin ga harkokin ci gaba da kuma zaman lafiya a duniya,

Wang Yi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a liyafar sabuwar shekara da aka shiryawa jakadun kasashen waje da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa, inda ya ce, tsarin diflomasiya na kasar, zai yi kokarin samar da yanayin da ya dace wajen zurfafa manufofinta na yin gyare-gayre tare da cimma manufar da kasar ke bukata.

Ministan ya ce, a shekara ta 2013, kasar Sin ta cimma nasarori masu muhimmanci a ayyukanta na diflomasiya, idan aka yi la'akari da matsayin ci gaban kasar a idon duniya da kuma tasirinta.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce, kasar ta Sin, ta kara bunkasa hadin gwiwa da sauran kasashe, taka rawar da ta dace wajen warware muhimman batutuwa, tare da imanin cewa, ci gaban kasar na Sin zai samar da muhimmiyar dama ga ci gaban zaman lafiya da makoma mai haske ga duniya.

A nasa jawabin, jakadan kasar Togo da ke nan kasar Sin, Nolana Ta-Ama, ya yaba da irin nasarorin da kasar Sin ta cimma a shekara ta 2013.

Sama da mutane 400 ne ciki har da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi suka halarci liyafar ta ranar Laraba da aka shirya a nan birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar Sin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China