Ita dai rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin zagaye na 15 ta kammala aikinta na tsawon watanni 8, kuma yanzu haka, sojojin Sin 118 daga cikinsu sun riga sun sauka a filin jirgin saman Xianyang dake birnin Xi'an na kasar Sin a ranar Jumma'a 9 ga wata.
Wannan rundunar soja ta tashi zuwa yankin Bukavu na kasar Kongo Kinshasa a watan Nuwamba na bara domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, a lokacin kuma, gaba daya hafsoshi da sojojin sun gudanar da aikin yadda ya kamata, tare da samun amincewar tawagar musamman ta MDD kan tabbatar da zaman lafiya a Kongo Kinshasa, da rundunonin sojan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, da kuma gwamnati da jama'ar wurin. (Fatima)