Babban taken taron shi ne zaman lafiya, bunkasuwa da kirkire-kirkire, wadanda suka shafi tsaron kasa da kasa a yayin da ake samun sauye-sauye a duniya. Li Yuanchao, mataimakin shugaban kasar Sin zai halarci bikin bude taron tare da yin jawabi.
Madam Hua ta kara da cewa, shugaba Ernest Bai Koroma na kasar Saliyo, shugaba Desire Bouterse na kasar Surinam, Dmitry Mezentsev, babban sakataren kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da wasu shugabannin kasashen duniya da kusoshin kungiyoyin kasa da kasa za su halarci taron, inda kuma jami'an gwamnatin kasar Sin da abin ya shafa da kwararrun da suka fito daga cikin gida da wajen kasar Sin za su halarta.
Taron dandalin tattaunawa kan zaman lafiya na duniya ya zama na farko da kasar Sin ta shirya wani babban taron kasa da kasa, wanda ba gwamnatin kasar ta shirya ba. Makasudin shirya taron shi ne samar wa masu ilmin manyan tsare-tsare da jami'an kungiyoyin nazari wani dandali don su tattauna yadda za a kara azama kan shimfida zaman lafiya da tsaro a duniya. (Tasallah)