Wannan rundunar soja ta hada da hafsoshi da sojoji 395, ciki har da wani rukunin injiniyoyi mai kunshe da sojoji 155, da wani rukunin kiyaye tsaro mai kunshe da sojoji 170, da kuma wani rukunin ba da jiyya mai dauke da sojoji 70. Za a kasa wannan rundunar sojan kashi biyu domin tafiya zuwa Mali a karshen watan Yuli da kuma farkon watan Satumba na bana, a kokarin daukar nauyin gyara hanyoyi da gadoji, da kiyaye sansanin soja, da ba da jiyya da sauransu.
Kafin wannan, sun riga sun koyi ka'idojin aikin kiyaye zaman lafiya, da samun horon fasahohin kiyaye zaman lafiya da yaki da ta'addanci da sauransu.(Fatima)