A cewar Madam Hua, kasar Sin a matsayinta na daya daga cikin kasashen dake da zaunannun kujeru a kwamitin sulhu na MDD, ta dade tana ma ayyukan kiyaye zaman lafiya goyon baya, har ma ta kasance daya daga cikin kasashen da suka tura sojoji mafi yawa domin aikin.
Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura jami'ai da 'yan sanda fiye da dubu 20 zuwa waje domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. A halin da ake ciki kuma, akwai jami'ai da 'yan sandan kasar Sin 1645 dake gudanar da ayyukansu a wasu yankuna guda 9 dake kasashe daban daban. Haka zalika, a cikin sahun kasashe masu tasowa, kasar Sin ita ce ta fi samar da kudi ga MDD don tallafawa aikin wanzar da zaman lafiya.
Madam Hua ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ta jagoranta, don samar da gudummawa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk duniya.(Bello Wang)