in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama dole a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin hadin gwiwa
2014-02-27 20:57:09 cri
Dangane da matakan da mahukuntan gwamnatin Abe Shinzo na kasar Japan suka dauka a kwanan baya, Yang Yujun, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayyana yau Alhamis 27 ga wata cewa, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 120 da barkewar yaki na farko a tsakanin kasashen Sin da Japan, haka kuma shekara ce ta cikon shekaru 100 da barkewar yakin duniya na farko, kuma shekaru 75 da barkewar yakin duniya na biyu. Abubuwan da suka faru a tarihi sun koyar mana darasi mai kyau, don haka dole ne a yi koyi da su. Har wa yau an sha wuya kafin aka samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, don haka ya zama dole a kiyaye su cikin hadin gwiwar kasa da kasa.

Mista Yang ya kara da cewa, a shekarun baya, masu tsattsauran ra'ayi na Japan sun juya baya sosai ga tarihi, sun kara yawan kayayyakin soja bisa hujjoji daban daban, a yunkurin da suke yi na canza sakamakon yakin duniya na biyu da kuma tsarin kasa da kasa bayan yakin, lamarin da wajibi ne kasashen duniya su yi taka-tsantsan a kai. An danka wa sojojin kasar Sin nauyin kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa, saboda haka ba za su yarda da sake abkuwar abubuwan tausayi a tarihi ba. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China