Ya zuwa daren ranar Talata 11 ga watan nan, jirgin saman kasar Malesiyan nan da ya bace ya zarta sa'o'i 90 ana neman sa. Yayin da kafofin watsa labarai ke ci gaba da bayyana halin da ake ciki.
Duk dai da cewa ba a sami wani ci gaba don gane da neman da ake yi wa wannan jirgi ba, a hannu guda rukunonin masu aikin ceto na kasa da kasa, na yin iyakacin kokarinsu, baya ga kyakkywan fata da al'ummar duniya ke yi ga mutane dake cikin wannan jirgin na tsira da rayukan su.
Kamfnain jiragen saman na Malaysiya ya bayyana cewa, ya zuwa karfi 11 na daren ranar Talata, an gudanar da aikin neman wannan jirgi a wurare da dama, ciki hadda gabashin tsibirin Malesiya, da yammacin yankin. Inda jiragen ruwa masu aikin ceto 42, ciki hadda na kasashen Sin, da Vietnam, da Singapore, da Amurka, da Austriliya da sauransu, da kuma jiragen sama 35.
Ban da batun neman wannan jirgi, ana kuma nazartar dalilin aukuwar hadarin, musamman ma kan ko lamarin na da alaka da harin ta'addanci. In da shugaban hukumar lura da sakwannin sirri ta Amurka Sue Brennan, ya bayyana cewa, mai yiwuya ne akwai wannan alaka, wanda hakan ya sa hukumarsa ke hadin gwiwa da hukumar bincike ta kasar FBI, da ma sauran hukumomin tsaro kan wannan batu.
A wani bangaren kuma hukumar 'yan sanda masu binciken manyan laifufuka ta kasa da kasa ta bayyana a ranar 11 ga watan cewa, tana ganin wannan hadari ba shi da alaka da harin ta'addanci, duba da dimbin shaidu da ta tattara a 'yan kwanakin nan. (Amina)