in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoma da makiyaya sun kulla yarjejeniyar sulhu a jihar Benue dake Najeriya
2014-04-07 16:47:17 cri

Fulani makiyaya da manoma a jihar Benue a Najeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin su bayan shekaru biyu da aka kwashe ana dauki ba dadi.

Bangarorin biyu sun amince da cewa, makiyayan za su ci gaba da kiwon dabbobinsu a duk fadin jihar amma kuma ya kamata su rika mutunta matsayin manoman jihar. Haka kuma sun amince da aka kafa kwamitin al'ummar Tibi da Agatu da makiyaya wadanda za su zakulo miyagu daga cikinsu.

An dai cimma wannan matsayi ne a wajen wani taron kwamitin shugaban kasa kan zaman lafiya a karkashin jagorancin mataimakin shugaban 'yan sanda na kasa, Michael Zoukumor da kuma shugaban kungiyar Miyetti Allah Alhaji Bello Abdullahi Bodejo.

Shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa, rundunar 'yan sanda za ta sa ido don ganin bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar, inda ya nemi hadin-kan kafafen yada labarai na ganin an shawo kan matsalar.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China