140402murtala.m4a
|
Daraktan yada labarun rundunar tsaron kasar, Chris Olukolade ne ya bayyana hakan, yana mai cewa lamarin ya auku ne a wani karamin gari, mai suna Mulai dake daf da birnin na Maiduguri.
Manjo-Janar Olukolade ya ce motoci uku daga cikin hudu, da suke dauke da bama-bamai sun yi fata-fata, sakamakon budewa wuta da sojojin suka yi kan maharan, lamarin da ya sanya bama-baman dake cikin motocin tarwatsewa.
Sojoji biyar sun samu raunuka, sai dai har zuwa yanzu ba'a tabbatar da adadin fararen hular da harin ya shafa ba, a cewar Olukolade.
Bisa labarin da muka samu, an ce, bama-baman sun fashe ne da misalin karfe biyu na ranar talata, a garin na Mulai, dake kusa da gidan rediyon Peace FM, wanda harin ya taba wani bangare na ginin harabar sa.
Garin Mulai na da nisan kilomita 5 ne kacal da cikin garin Maiduguri, kuma gari ne da daruruwan mutane suke hada-hada da kai-kawo a kullum, tun bayan da aka kafa wani babban gidan man fetur, mallakin gwamnatin tarayya a cikin sa.(Murtala)