A cewar ministan ma'aikatar watsa labarun kasar Mr. Labaran Maku, shekaru 15 ke nan, da fidda cikakken rahoton matsayin GDPn kasar, sai dai yanzu haka ana shirin sauya wannan tsari, ta yadda za a rika fidda rahoton kididdigar bayan kowane shekaru biyar. Wanda hakan zai bada damar sanin sassan tattalin arziki dake samun ci gaba, da kuma masu fuskantar kalubale.
Bayan kammalar aikin hada wannan rahoto, wanda wasu cibiyoyin bincike na kasar, da hadin gwiwar kwararru daga ketare ke aiki a kai, a cewar Mr. Maku, al'ummar Najeriya za su samu cikakken bayani game da matsayin tattalin arzikin kasar.
Bisa hasashen da aka yi a bara, mizanin na GDP a Najeriya na iya kunsar dalar Amurka miliyan dubu 451. Inda sashen noma ya samar da kaso mafi tsoka na kashi 49 bisa dari, yayin da harkar bada hidima ta samar da kaso 30, sai sashen masana'antu mai kaso 15, yayin da na albarkatun mai ke da kaso 15 bisa dari. (Saminu Hassan)