in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Yobe a Najeriya ta shirya tsaf don gina hanyoyin gwamnatin tarayya dake jihar
2014-03-29 16:49:01 cri

Gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, ta shirya tsaf don gina dukkanin illahirin hanyoyin gwamnatin tarayya dake kowane sashi na jihar.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam, a yayin da yake duba ayyukan da gwamnatinsa ta bayar na sake gina hanyoyin motar da suka tashi daga garin Potiskum zuwa Garin Alkali, mai tsawon kilomita 155, a kan kudi Naira Biliyan 7.6, da kuma wacce ta tashi daga garin Gashuwa zuwa garin Yunusari mai tsawon kilomita 31, da kuma hanyar nan mai matukar tarihi wacce ta tashi daga Kanemma zuwa garin Machina mai tsawon kilomita 300, wacce babu ita a da, amma gwamnatin jihar ta Yobe ta bada aikinta a yanzu domin amfanin al'ummar jihar, da ma kasa baki daya.

Gwamna Gaidam ya kara da cewa, samar da hanyoyi ga al'umma yana kan gaba, wajen habaka tattalin arzikinsu musamman ma ganin cewar mafi yawan al'ummar jihar manoma ne, da makiyaya da masunta, wadanda a kullum ke da bukatar hanyoyin da za su rika bi domin kai kayayyakin su zuwa kasuwanni a cikin jihar da kuma wasu sassan kasar baki daya.

Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan ma'aikatar ayyuka dake jihar Yobe Alhaji Lawan Shettima Ali, cewa ya yi a saninsa kusan a dukkan fadin kasar, gwamnatin jihar Yobe ce kawai ta ke gina hanya mai tsawon kilomita 300, ba tare da neman tallafi ba, duk da cewar ba hakkinta ne yin hakan ba.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China