in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Duniya da asusun IMF da kuma Bankin Raya Afrika sun amince da sabon GDPn Nigeriya
2014-04-07 16:08:05 cri
Asusun ba da lamuni na duniya IMF da wasu manyan cibiyoyin hada hadan kudin na duniya guda biyu sun amince da sabon hasashen GDP da Nigeriya ta fitar wanda ya sa ta zama kasa mai girman tattalin arziki a nahiyar baki daya, in ji wani jami'in asusun a jiya Lahadi.

Gene Leon, babban wakilin asusun a Nigeria ya yi bayanin cewa a madadin manyan cibiyoyin hada hadan kudin na duniya uku wato Bankin Duniya, Bankin Raya kasashen Afrika da kuma asusun ba da lamuni ta duniya IMF yana tabbatar da cewa sun amince da sabon hasashen GDP kuma sun goyi bayan Nigeriya a kokarinta wanda hakan zai kara habaka tattalin arzikin kasar.

A bisa sakamakon da aka fitar na bara GDPn na matsayin dala biliyan 509.9 ya dara na kasar Afrika ta kudu, abin da ya sa ya zama a kan gaba a nahiyar baki daya. Wannan sabon adadin da cibiyar kididdiga ta kasar ta fitar ya nuna cewa kasar da take kan gaba a samar da man fetur a Afrika yanzu ita ce ta 26 a duniya.

Ministan tsare tsaren tattalin arzikin kasar Ngozi Okonja-Iweala ta jaddada muhimmancin yin gyaran fuska a yadda ake tafiyar da tattalin arzikin wanda yanzu haka yawan GDP na kowane dan kasa ya kai dalar Amurka 2,688, abin da ya sa kasar ta zama ta 121 a duk duniya.

Karuwan GDP na Nigeriya na bara na nufin cewar hauhawar kasar a tattalin arziki zai yi kasa a bana amma zai kuma iya rage yawan bashin da ake binta dangane da adadin GDP nata da yake a matsayin kashi 21 a cikin 100. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China