koubo2.m4a
|
A cikin wata sanarwar da aka fitar a Abuja, babban birnin Kasar ,babban jami'in sashin watsa labarai na rundunar tsaron kasar manjo-janar Chris Olukolade ya bayyana cewa, matakan sojan da ake dauka zasu kawo karshen yawan kashe-kashen da ake yi, da kuma hasarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a wadannan wurare.
Mista Olukolade ya ce an riga an jibge sojojin sama, da 'yan sanda da kuma jami'an tsaro da dama a Benue, Nassarawa da Filato, a wani kokari na farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wuraren da suke zaune cikin fargaba saboda rashin zaman lafiya.
Janar Olukolade ya kuma yi kira ga mazauna wadannan jihohin uku da su bada hadin-kai ga sojojin gwamnatin, ta kokari samar da bayanai masu amfani domin taimakawa aiwatar da matakan tsaro yadda ya kamata.(Murtala)