in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Borno a Najeriya ta dauki nauyin mata 30 don karatun ilimin likita a kasar Sudan
2014-04-03 16:01:45 cri
Gwamnatin jihar Borno, dake Arewa maso Gabashin tarayyar Najeriya, ta dauki nauyin tura matan jihar su 30 zuwa kasar Sudan, domin karatun ilimin aikin likita.

A kwanan baya ne dai gwamna jihar Kashim Shettima, ya jagoranci wani bikin ban kwana da daliban a gidan gwamnatin jihar dake Maiduguri, kafin daga bisani su tashi zuwa kasar ta Sudan.

Gwamnatin jihar dai za ta biyawa kowace daliba dalar Amurka 9,500, kwatankwacin naira miliyan daya, da dubu dari biyar, a kowane zangon karatu.

Haka kuma gwamnatin ta baiwa dukkanin daliban dala 1000, a matsayin kudin kashewa, sai kuma dala 200, da zata rika aika musu a kowane wata. Kafin tashin daliban, gwamnatin ta kuma rabawa kowaccen su na'ura mai kwakwalwa domin taimaka musu wajen karatun su.

Har wa yau gwamnan jihar ya yi alkawarin ziyartar su, yayin da suke ci gaba da karatu a kasar ta Sudan.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China