in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta kame wasu fina-finan da aka fassara su cikin harshen Hausa batare da izini ba
2014-03-30 17:36:08 cri

A ranar Asabar 29 ne hukumar tace fina- finai ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta gudanar da wani samame inda ta samu nasarar kame wasu dillalan sayar da fina- finan kasashen Sin da Amurka da kuma Indiya da aka fassara su cikin harshen Hausa batare da izini ba.

Babban sakataren hukumar Alhaji Ahmed Dahiru Beli shi ne ya jagoranci samamen bisa rakiyar wasu jami`an hukumar da kuma jami`an tsaro, inda aka kame wasu dillalai guda biyu da suke sayar da wadannan fina- finai da aka fassara su cikin harshen hausa ba tare da la`akari da tanade tanaden dake tattare da addini da kuma al`adar hausawa ba.

A kalla fina-finai sama da dubu daya aka kwace daga wurin wadannan dillalai, da aka samu a shaguna da kuma bakin manyan titunan dake cikin birnin Kano.

Da yake jawabi ga manema labarai, babban sakataren hukumar Alhaji Dahiru Beli ya ce irin kallamomin Hausa da aka yi amfani da su wajen fassara wadannan fina- finai ya saba da tsarin al`ada da addinin islama.

Yace a binciken da hukumar ta gudanar , masu wannan fassara suna yi ne batare da izinin ainihin kamfanonin da suka shirya fina finan ba, inda yace wannan wani karan tsaye ne ga dokokin shiryawa da kuma dillancin fina- finai a tarayyar Najeriya.

Yacigaba dacewa akwai kalmomin batsa da yawa a cikin fina- finan kuma masu fassarar basu yi la`akari dasu ba haka suka fassara kuma suke yadawa a kasuwanni.

Alhaji Dahiru Beli ya kara dacewa aka sarin masu wannan fassara suna zaune ne a jihar Plato da kuma jihar Kano, kuma ana nan ana kokarin kamo su domin gurfanar dasu gaban kuliya.

Yace tuni hukumar ta gabatar da wannan korafi ga hukumar kare hakkin mallaka ta tarayyar Najeriya domin gaggauta yiwa tufkar hanci, kasancewar itace ke da alhakin dakatar da yaduwar irin wadannan fina- finai a tarayyar Najeriya.

Su dai wadannan dillalai biyu tuni aka yanke masu hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kurkuku ko biyan tarar naira dubu 150.

Daga karshe ya gargadi masu wannan sana`a ta sayar da fina- finai a jihar Kano dasu rinka kiyaye wad a irin fina- finan da suke sayarwa, domin tabbatar da ganin basu saba da tsarin tarbiyar bahaushe da kuma tsarin addinin musulunci ba.

Yace hukumar zata kara sanya idanu sosai a kasuwannin dake cikin birnin Kano da kewaye da kuma yankunan karkara don tabbatar da ganin cewa an shawo kan wannan matsala.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China