Emefiele, wanda wa'adin aikinsa zai fara daga ranar 2 ga watan Yunin dake tafe, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba. Yana mai cewa manufofin kare tattalin arziki, da samar da ci gaba mai dorewa ne za su zamo a sahun gaba cikin ayyukan da yake fatan aiwatarwa a zangon aikinsa.
Kazalika, sabon gwamnan mai jiran gado ya ce bankin na CBN zai yi iyakacin iyawa wajen kare bukatun masu ruwa datsi a fannin tattalin arziki, ta yadda zai yi cikakkiyar gogayya da takwarorinsa na sauran kasashen duniya.
A Larabar makon jiya ne dai majalissar dattijan kasar ta tantance sabon gwamnan bankin, bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya mika sunansa gaban majalissar. Zai kuma maye gurbin tsohon shugaban babban bankin Sanusi Lamido Sanusi, wadda aka dakatar daga aiki bisa zargin aikata wasu laifuka masu alaka da karya dokokin aiki. (Saminu Hassan)