in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnati jihar Katsina ta Najeriya zata baiwa mutanen da hari ya rutsa da su tallafin kudi
2014-04-05 15:44:40 cri

Gwamnatin jihar Katsina dake arewacin tarayyar Najeriya zata bada tallafin naira miliyan 100, ga wadanda harin 'yan bindiga ya rutsa da su a wasu kauyukan jihar a watan da ya gabata.

A cewar gwamnatin jihar, tallafin wani mataki ne na saukakawa wadanda harin ya afkawa radadin halin da suka samu kansu a ciki.

Kamar yadda wata sanarwar da mai taimakawa gwamnan jihar na musamman ya fitar ta ce, cikin wadanda za'a bawa tallafin har da 'yan sanda uku da suka rasa rayukansu yayin tarzomar, da kuma babban jami'in 'yan sandan yankin Faskari da ya samu raunuka.

Sama da mutane 100 ne dai suka rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka, sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a jihar ta Katsina a kwanan baya. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China