0330murtala222.m4a
|
Wannan abu ya faru ne da misalin karfe 7 da minti 15 na safiyar nan. Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar hukumar tsaron farin kaya ta SSS, Marilyn Ogar ta bayyana cewa, jami'an dake kula da 'yan ta'addan da ake tsare da su ne suka je kai musu abinci, sai su wadanda ake tsare da su suka auka musu, inda nan take suka yi nasarar kwacewa, tare da fara harbe-harbe. Matakin da ya sanya aka gayyato sojoji, kafin 'yan ta'addan su yi wata barna, wanda kuma a cewar ta wannan ne dalilin karar harbe-harben da aka ji.
Madam Marilyn Ogar ta kara da cewa, hakan wani yunkuri ne na karya wurin da suke tsare, da nufin su tsere, amma ba su samu nasarar hakan ba.
Game da abin da ya faru, mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin watsa labarai Mr. Reuben Abati ya fitar da wani gajeren jawabi, inda ya bayyana cewa, harbe-harben ya faru ne sakamakon wani yunkurin tserewa, da wasu 'yan ta'adda da ake tsare da su a hedkwatar SSS suka yi, wanda hakan ya haifar da harbe-harben, da ma tururuwar jami'an tsaron sojoji da shawagin kananan jiragen yaki a yankin.
Haka kuma cikin jawabin, Mr. Abati ya ce harbe-harbe ba su shafi fadar shugaban kasa ta Aso Villa ba, haka kuma shugaban kasa Goodluck Jonathan yana nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Wata majiya ta shaida mana cewa, yayin balahirar jami'an SSS din, sun harbe wadanda ake tsare da su 18, da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne dake kokarin tserewa.(Murtala)