A cikin sakon, Mr. Xi ya bayyana cewa, tashar bincike ta Taishan da sauran tashoshin bincike na Changcheng, Zhongshan, da Kunlun da ke Antatika da tashar bincike ta Huanghe da ke yankin Aktik sun zama dandalin binciken yankunan da suka raba duniya na kasar Sin, kana sun zama wata kafar yin mu'amalar kimiyya da kasashen duniya.
Mr. Xi ya bayyana cewa, ya yi imani cewa, bisa kokarin masu nazarin yankunan da suka raba duniya na kasar Sin, sha'anin nazarin yankunan da suka raba duniya na kasar Sin zai kara ba da gudummawa wajen kawo alheri ga jama'a.(Bako)