A yayin taron da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ya shugabanta, an nuna cewa, a shekarar 2013 da ta gabata, sakamakon gazawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya ya sa kasar Sin ta fuskanci matsalar raya tattalin arzikinta. Ban da haka, kasar Sin ta samu yawan abkuwar bala'u daga indallahi da dama tare da fuskantar hali mai yamutse, amma a karkashin shugabancin JKS, jama'ar Sin sun daidaita irin wadannan kalubaloli cikin nitsuwa, sun jure wahalhalu da dama, sun cimma burinsu na raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar. Sa'an nan kuma kudin shigarsu ta yi ta karuwa. Kasar Sin ta samu ci-gaba wajen kyautata tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki, tare da samun bunkasuwar sha'anin jin dadin rayuwar jama'a. Ana iya cewa, kasar Sin ta samu sabbin nasarori a fannonin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, da kuma raya kasar ta hanyar gurguzu daidai da zamani.
Taron ya jaddada cewa, a bana, kasar Sin za ta ci gaba da fuskantar wani irin yanayi, don haka tana bukatar tinkarar kalubaloli da za su biyo baya da kuma zarafi a lokaci guda. Ya zama dole ta yi hangen nesa, ta yi taka-tsantsan kan abubuwan da za su kawo mata illa, a kokarin ci gaba da raya kanta yadda ya kamata. (Tasallah)