in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Rasha sun tattauna game da dangantaka tsakanin kasashen biyu
2014-03-05 10:15:44 cri

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin game da dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a kasar Ukraine.

Shugabannin biyu dai sun tattauna a birnin Sochi ne ba da dadewa ba, abin da ya kasance mafarin dangantakar kasashen biyu a wannan shekara, inda sassan biyu ke kara yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a bangaren manyan ayyuka.

Shugaba Xi ya ce, a halin yanzu, halin da ake ciki a Ukraine mai rudawarwa ne sosai, kuma zai tasiri ga shiyyar, da ma duniya baki daya. Kasar Sin ta yi imanin cewa, Rasha za ta hada kai da sauran sassan da abin ya shafa don warware batun ta hanyar siyasa, ta yadda za a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyyar da kuma duniya baki daya.

Shugaba Putin ya sanar da shugaba Xi game da halin da ake ciki a kasar ta Ukraine, matsayin Rasha game da batun da kuma matakan da Rashan ke dauka don warware rikicin.

Shugaba Putin ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin ta'addancin da ya faru a Kunming da ke lardin Yunnan na kasar Sin, inda ya bayyana goyon bayansa ga kasar Sin a kokarin da take na yaki da ayyukan ta'addanci.

Shugaba Xi yana sa ran ba da dadewa ba shugaba Putin zai kawo ziyara kasar Sin, inda ya bayyana kudurinsa na ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China