Shugaba Xi ya bada shawarar cewa, ya kamata da farko manyan jami'an kasashen biyu su kara yin mu'amala tsakaninsu.sannan kuma su kara hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, manyan kayayyaki na sufuri da sauransu. Sai kuma shawarar sa na uku da ya ce su kara hadin gwiwa wajen kyautata harkokin duniya da na shiyya-shiyya, a kokarin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
Bayan haka, shugaba Xi ya kara da cewa, kasar tana goyon bayan kasashen Afirka wajen samun wata hanyar bunkasuwa data dace da yanayin da suke ciki.
A cewar shi kasar tana dora muhimmanci kan koyar da fasahohi ga kasashen Afirka, a kokarin cimma burin ganin sun samu bunkasuwa da kansu. Don haka Sin na fatan sa kaimi ga bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki tare da kasar Senegal.
A nasa bangare kuma, shugaba Sall ya bayyana cewa, Senegal na fatan kara hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannonin makamashi, manyan kayayyaki da zasu amfani jama'a, kayan amfanin gona da sauransu. Kuma kasar tana maraba da ganin Sin ta yi kokarin kafa cibiyar al'adun ta a Senegal tun da wuri. (Fatima)