Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, ya ce, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, zai gana da takwaransa na Amurka Barack Obama, gabannin taron tattauna kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliya, wanda za a yi a kasar Netherlands.
Mr. Li, wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, ya kara da cewa, ganawar da shuwagabannin za su yi, za ta zamo ta farko a tsakanin su cikin wannan shekara. Za kuma su yi amfani da wannan dama, wajen tattauna lamurran da suka shafi ci gaban alakar dake tsakanin kasashen nasu.
"Kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da Amurka, a kokarin da ake yi na samun nasarar tattaunawa kan batun makamashin nukiliyar duniya, baya ga kokarin da take yi na habaka dangantakar diplomasiyyarta, da sauran kasashen duniya." A kalaman Mr. Li.
Baya ga halartar wannan taro a ranekun 24 da 25 ga watan nan na Maris, a birnin Hague na kasar ta Netherlands, shugaba Xi zai kuma ziyarci kasashen Netherlands, da Faransa, da Jamus da kuma Belgium.
Haka zalika, zai kai ziyara helkwarar hukumar UNESCO ta MDD, da kuma helkwatar kungiyar tarayyar Turai ta EU. (Saminu)