Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron farko na hukumar tabbatar da tsaron yanar gizo da bayanai, wanda aka gudanar a ranar 27 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi.
Cikin jawabin nasa shugaba Xi dake matsayin jagoran wannan hukuma ya karfafa batun kudurin da gwamnatinsa ke da shi, na sanya kasar Sin zama a sahun gaba a fannin fasahar intanet. Ya ce dole ne a samar da fasahohi masu inganci, da ba da hidimar bayanai a dukkanin fannoni, da kuma samar da muhimman na'urorin yada bayanai domin cimma wannan buri.
Shugaban ya ce samar da kwararru a fannin tabbatar da tsaron shafukan intanet da na bayanai, da kara yin mu'ammala da hadin gwiwa tsakanin Sin da bangarori duniya daban daban a wannan fanni, na da matukar muhimmanci wajen daga matsayin kasar ta Sin a wannan fage.(Danladi)