Shugaba Xi, ya yi wannan kira ne a Asabar din nan, yana mai umartar ma'aikatar waje, da kuma ofisoshin jakadancin kasar sa, da hadin gwiwar kasashen da lamarin ya shafa, da su kara azamar gano inda wannan jirgi ya shiga. Ya ce ya zama wajibi, a yi duk mai yuwuwa, domin fuskantar yanayin da za a iya gamuwa da shi, da zarar an gano wannan jirgi.
Shi dai wannan jirgi kirar Boeing 777-200, ya taso daga birnin Kulala Lumpur na kasar ta Malesiya ne, zuwa nan birnin Beijing da sanyin safiyar Asabar din nan, ya kuma kamata ya iso birnin na Beijing da misalin karfe 6:30 na safe, amma kawo lokacin gabatar da labaran nan, ba a samu labarin inda ya shiga ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan jirgi, na dauke da fasinjoji 'yan kasashe da dama, ciki hadda 'yan asalin kasar Sin 154. (Saminu Alhassan)