Taron wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranta, ya amince da muhimmin kundin aikin da kwamitin zai gudanar na wannan shekara.
Bugu da kari, taron ya samu halartar Li Keqiang, Liu Yunshan da Zhang Gaoli da dukkan mambobin hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS.
Shugaba Xi ya bukaci shugabanni da su mayar da hankali kan abubuwan da ke kunshe cikin kudin kan wasu sassa na musamman kana su fito da bayanai ga jami'an da abin ya shafa da kuma lokacin da aka tsara.
Ya kuma jaddada cewa, wajibi ne a gudanar da aiki kamar yadda doka ta tsara yayin aiwatar da wadannan gyare-gyare, sannan wajibi ne duk wasu manyan canje-canje su dace da doka. (Ibrahim)