Ranar Jumma'a 7 ga wata, hedkwatar MDD, ta yi bikin taya murnar sake zagayowar ranar mata ta duniya, kwana guda kafin ranar da aka kebe domin bikin . Tare da yin kira da a yi kokarin samarwa mata daidaito, da tabbatar da kare hakkokinsu. A bana taken ranar shi ne "Samarwa mata daidaito ci gaba ne ga Bil Adama",
A sakon sa na wannan rana, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon, cewa ya yi, kasashen da suke samar da daidaito tsakanin jinsuna, na sahun gaba a fannin bunkasuwar tattalin arziki, wanda hakan ya zama wata alama ta bunkasar rayuwar Bil Adama.
Shima a nasa tsokaci don gane da wannan rana, shugaban babban taron MDD karo na 68 John Ashe, cewa ya yi, kamata yayi maza su shiga aikin samarwa mata daidato. Ya ce kasancewar maza ne kan shugabanci fannonin rayuwa daban-daban, ciki hadda iyali, da al'umma, da gwamnatoci, da harkokin cinikayya, da ma kasashe da duniya baki daya. Hakan ya sa karfinsu zai taimaka, wajen samar da daidato tsakanin jinsunan Biyu. (Amina)