A Gurin babban taron MDD da ya gudana a birnin New york ranar 28 ga watan satumba dangane da cututuka marasa yaduwa, inda aka sa ran ganin wasu matan shugabannin kasashen Afirka da masu bincike za su samar da wata sanarwa kan yadda za a yi kokarin shawo kan cutar dajin mata a Afrkia a wajen taron da ake gudanar a Addis Ababa.
A cewar wata babbar darakta ta wata kungiya mai zaman kanta ta Nigeria mai suna 'Nicky breast cancer foundation', kuma wadda ta shirya wannan taro, Ginbiya Nicky Onyeri, ta ce, makasudin taron shine dan a wayar da kan shugabanni da nuna wa al'umma mahimmancin wannan cuta da illa da take da ita a Afrika
Nicky ta shaida cewa, taron da za a yi zai mika bayanai kan yadda za a fifita maganar sankarar mama da ta mahaifa a cikin batutuwan da za a tattauna babban taron MDD da za a gudanar a nan gaba.
Nicky ta kara da cewa cutar dajin mama da ta mahaifa tana kashe matan Afrika dan haka ta bukaci al'umma da su wayar da kai a kan matsalar wadda za a iya daidaita ita .(Salamatu).