A wannan rana, kwamitin sulhu ya yi muhawara kan batutuwan mata da zaman lafiya da tsaron kai, tare da zartas da wata sanarwar shugaba. Sanarwar ta jaddada cewa, kamata ya yi a sa kaimi kan kiyaye hakkokin mata, a aiwatar da dokokin jin kai da na kiyaye hakkokin dan Adam na kasa da kasa a lokacin da ake fuskantar tashin hankali da kuma bayan tashin hankali, sa'an nan a karfafa gwiwar mata da su kara shiga ayyukan yin rigakafi da daidaita tashin hankali da raya kasa cikin lumana, tare da tabbatar da rashin nuna bambanci a tsakanin maza da mata cikin kungiyoyin musamman da MDD ta tura a sassa daban daban na duniya.
Haka zalika, Li Baodong, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya jaddada a yayin muhawarar da aka yi a wannan rana da cewa, kamata ya yi kwamitin sulhu ya himmantu wajen hana da kuma rage illar da tashin hankali kan yi wa mata, ya kuma yi kira da a yi amfani da basirar da mata suke da ita wajen kiyaye zaman lafiya da tsaron kai a duniya, tare da kiyaye hakkokinsu yadda ya kamata. (Tasallah)