in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron koli na matan kasashen Larabawa da kasar Sin na shekarar 2012 a kasar Masar
2012-11-16 13:17:59 cri

A ranar 15 ga wata, an yi taron koli na matan kasashen Larabawa da na kasar Sin na shekarar 2012 a birnin Alkahira da ke kasar Masar, a sa'i daya kuma, an bude taron mata masu harkar masana'antu na kasashen Larabawa da kasar Sin karo na farko a wurin. Shugabar kwamitin harkokin mata na kasar Masar Mervat Talawy da jakadan Sin da ke kasar Masar Song Aiguo sun halarci taron.

Taken taron koli na wannan karo shi ne, "Dama da kalubale, da kuma matakan da matan kasashen Sin da Larabawa za su dauka". Sarakunan kasashen Larabawa da matar jiga-jigan 'yan siyasa na kasashen Larabawa da na kasar Sin, 'yan siyasa da jami'an kungiyoyin mata da kwararru a fannin mata har ma da mata masu harkar masana'antu sun halarci taron, inda suka tattauna sabbin manufofin da za a aiwatar wajen warware batutuwan mata na kasashen Sin da Larabawa da kuma kara sa kaimi ga harkokin mata na wadannan kasashe don su samu ci gaba.

Taron koli na matan kasashen Sin da Larabawa, kungiyar kula da harkokin mu'amala tsakanin kasashen Sin da Larabawa ce ta shirya, wanda ya zama wani muhimmin tsarin hadin gwiwa, wajen yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin mutane ko kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Sin da kasashen Larabawa, da nufin ci gaba da inganta dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunta tsakanin kungiyoyin mata na kasashen Sin da Larabawa, gami da kara fahimtar juna tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China