in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a dauki matakan gaggawa domin kare 'yancin mata.
2012-02-24 11:04:27 cri
A lokacin wata mahawara a zauren MDD a ranar Alhamis, wakilin kasar Sin a zauren, ya yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar da a tsare yancin mata tare da bukatunsu ta hanyar daukar matakai na gari na gaggawa. A lokacin da ya ke jawabi a gaban kwamitin kan mahawara dangance da mata, zaman lafiya da tsaro, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a zauren MDD, Wang Min ya ce, kasar Sin ta yi allah wadai da dukan irin hargitsin da mata ke samun kansu a lokutan yake-yake tare da yi musu fyade.

Ya furta cewa ,"domin kawar da wannan matsala da rage wahalhalun da mata ke fuskanta a lokacin tashe-tashen hankali, da farko sai mun hana wanzuwar yaki, da kuma rage abkuwar tashe-tashen hankali.

Wang ya ce, gwamnatoci na da nauyin farko na bada kariya ga mata da kuma gwagwarmayar kawar da yi musu fyade, it kuma hukumar kasa da kasa na iya kawo taimakon da ya kamata, wanda ya zo daidai da dokokin tsarin MDD, tare da darata yancin kasashen da lamarin ya shafa.

Buga da kari, a koye babban muhimmanci da a karfafa mata wajen halartar lamuren kawo zaman lumana domin su kawo na su kokari. (Abdou Halilou).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China