Cikin jawabinsa, Mista Ban ya ce, ana kai hari, fyade, da kisan miliyoyin 'yan mata a wurare daban daban na duniya, lamarin da ya kasance masu aikata hakan suna cin karen su babu babbaka wajen keta hakkin bil Adama. Sai dai kuma wadanda suka aikata laifi su kan samu damar tsallake hukunci,sakamakon al'adar kare masu aikata laifi wadda ta sa 'yan mata suke jin tsoron fadin abubuwan da aka yi musu.
A cewar Mista Ban, kungiyar hana cin zarafin mata ta majalisarsa tana kokarin neman janyo hankalin gwamnatocin kasashe daban daban, da kungiyoyin kasa da kasa da na jama'a, kafofin watsa labaru da dai sauransu, domin su ma su shiga wannan aiki. Wani binciken da kungiyar ta yi ya sheda cewa matasa da yawa sun yi kira da a kara mai da hankali kan kare 'yan mata, da yada ra'ayin tabbatar da hakkin bil Adama, gami da hada kan bangarori daban daban domin taimakawa matan da aka ci zarafinsu. (Bello Wang)