in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar jami'ar kasar Sin ta kai ziyara a kasar Aljeriya
2012-11-25 16:41:19 cri
Madam Chen Zhili, mataimakiyar shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma shugabar kungiyar 'yan mata ta kasar, wadda ke ziyara a kasar Aljeriya, ta gana da shugabannin kungiyar 'yan matan kasar Aljeriya a ranarjiya asabar 24 ga wata, kana ta yi hira da wasu sanannfitattun 'yan mata na kasar, wadanda suka kasance tsoffin sojoji, 'yan majalisa, jami'an gwamnati, da dai makamantansu.

A yayin ganawar, Madam Chen ta ce, akwai zumunci mai zurfi a tsakanin kasar Sin da kasar Aljeriya, bayan haka kuma kasashen 2 sun kara hada hadin kansu a shekarun baya, sa'an nan ta fuskar batun da ya shafi babbar moriyar kasar Sin, Aljeriya ta kan ba kasar Sin goyon baya sosai. Saboda haka, kasar Sin tana ganindaukar huldar dake tsakanin kasashen 2 da muhimmanci ainun, kana za ta ci gaba da kokarin hadin kai tare da kasashe daban daban, ciki har da kasar Aljeriya, bisa manufofi 5 na zama tare cikin lumana.

Haka zalika, a cewar Madam Chen, amincin da ya kasance tsakanin matan kasashen 2 ya zama wani muhimmin dalilin da ya taimakawa kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2, don haka kasar Sin na son ci gaba da mu'amala da hada kai tare da 'yan matan kasar Aljeriya, ta yadda za a samu damar kara imani zumunci a tsakaninsu, da taimakawa karfafa huldar aminci da hadin kai cikin aminci a tsakanin kasashen.

A nata bangare, Madam Hafsi, shugabar kungiyar 'yan matan kasar Aljeriya, ta ce, tawagar 'yan matan kasar Sin da sukenke kawo ziyara a kasar Aljeriya ne a lokacin da ake bikin murnar cika shekaru 50 da samun 'yancin kan kasar, da ma cika shekaru 54 da kulla hulda a tsakaninta da kasar Sin. Shi ya sa ziyarar tasu kena da muhimmanci da ma'ana, musamman ma a fannin kara dankon zumunci tsakanin 'yan matan kasashen 2, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen.

Sa''an nan sHaka kuma Sshugabar kungiyar 'yan matan kasar Aljeriya ta nunamika godiyar ta ga kasar Sin kan taimakon da take ba Aljeriya a kokarinta na samun 'yancin kai, da raya kasa. HakatTa kuma, takara yi godiya ga kungiyar 'yan matan kasar Sin, wadda ta taimaki Aljeriya wajen kula da mata da yaranta. Ta ce tana fatan ganin manyan kusoshinJjami'an Aljeriya da Sin da 'yan matan kasashen 2 su kara musayar ra'ayi, da hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.

A wajen taron, an yi tattaunawa kan yadda za a iya tabbatar da hakkin 'yan mata, da kara sanyamara masu baya don su shiga harkokin siyasa, da sa kaimi ga musayar ra'ayi da hadin kai tsakanin 'yan matan bangarorinkasashen 2, da dai makamantansuabin da ya shafi hakan, inda sShugabannin matan kasashen biyu suka cimma ra'ayi daya kan matakan da za a dauka don sanya kasashen Sin da Aljeriya su kara yi mu'amala da hadin gwiwa ta fuskar ayyukan kula da 'yan mata, abin da ya sa har ma Madam Chen Zhili, da Madam Hafsi, a madadin kungiyoyin 2 nasuke taimakawa 'yan mata, sukainda , suka kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China