in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sa himma wajen samar da guraben aikin yi ga mata da raya harkokin kiwon lafiya gare su
2012-03-10 21:16:50 cri
A ranar 9 ga wata da dare, yayin da babbar sakatariya ta hadaddiyar kungiyar mata ta kasar Sin Cui Yu ke zantawa da wakilinmu game da "Ci gaba da Sin ta samu wajen raya harkokin mata da yara cikin shekaru 10 da suka gabata", ta ce, hadaddiyar kungiyar mata ta Sin ta gudanar da manufofi da dama, don sa kaimi ga mata su samu guraben aikin yi, a sa'i daya kuma, da kara karfi wajen ingiza aikin kiwon lafiya ga mata a kauyuka.

Bisa alkaluman da aka samu, an ce, a shekarar 2010, yawan matan kasar Sin da suka samu guraben aiki yi ya kai kashi 46 cikin 100 a yawan ma'aikatar kasar. Haka kuma, Madam Cui Yu ta gabatar da cewa, don kara samar da guraben aikin yi ga mata, hadaddiyar kungiyar harkokin mata ta inganta hadin gwiwa da hukumar kula da jin dadin jama'a, da ma'aikatar kudi ,da bankin tsakiya na Sin, kuma sun gabatar da manufofi na samar da kudin bonas ga mata da suka samun rancen kudi kalilan.

Madam Cui Yu ta ce, ta hanyar ba da rancen kudi kalilan ga mata a birane da kauyuka, an kara musu goyon baya don su samu guraben aikin yi, haka kuma, gwamnatin kasar ta biya kudin ruwa da suka ci ba tare da biyan kudin ko sisi ba. A sa'i daya kuma, a ko wace shekara, kasar Sin ta kan horar da mata da yawansu ya kai miliyan 5 a kauyuka musamman ma, wadanda suke cikin kangin talauci.

Haka kuma, a shekarar 2009, hadaddiyar kungiyar mata ta Sin ta hada kai da ma'aikatar kiwon lafiya ta Sin, don duba lafiyar jiki musamman ma wajen gujewar sankarar mahaifa da ta mama ga mata a kauyuka.

Bisa labarin da aka samu, an ce, yanzu, kasar Sin ta riga ta duba lafiyar jikin mata a kauyuka da yawansu ya kai miliyan 12 don gujewar sankarar mahaifa da ta mama.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China