A shekarar 2001, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar da wani shirin kyautata zaman rayuwar 'yan mata, a shekaru 10 da suka wuce, gwamnatin kasar ta kara mai da hankali kan harkokin 'yan mata, da kara zuba jari, tare da yin furfoganda, don sa kaimi ga aiwatar da shirin.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, shekaru 19 da suka gabata sun kasance lokaci mafi kyau wajen raya zaman rayuwar 'yan mata. An kara ba da tabbaci ga zaman 'yan mata, da kara kyautata zaman rayuwar 'yan mata da talauci ya addaba, kuma yawan 'yan mata wadanda suka shiga siyasa da neman ilmi ya karu sosai. Ban da haka kuma, gwamnatin ta kara kyautata dokoki masu kare 'yan mata, an kuma kara samun daidaito a tsakanin maza da mata.(Abubakar)