Hajiya Zainab Maina ta fadi haka ne a yayin da take tattaunawa da wakilin CRI a ranar8 ga wata, inda ya ce, gwamnatin Nijeriya tana mai da hankali kwarai kan harkokin mata, musamman duba da irin taimakon da suke bayarwa ta fannin bunkasuwar al'umma, dan haka gwamnati ta sanya wasu nagartattun mata da su zama ministoci a gwamnatin tarayya da kuma kwamishinoni a jihohi.
Hajiya Zainab Maina ta ci gaba da cewa, kasar Sin ita ma ta samu ci gaba sosai game da inganta harkokin mata, sabo da haka Nijeriya ke koyi da kasar ta Sin, kuma acewarta kasashen biyu sun hada kai sosai a wannan fanni. Kasashen Nijeriya da Sin na dada karfafar juna a harkokin da suka shafi kasa da kasa, kamar a MDD inda suke kara bayyana bukatu da matsayin mata a idon duniya.(Dan Ladi)